1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Euro 2024: Aski ya zo gaban goshi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LMJ
July 9, 2024

A wannan makon za a gudanar da wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai Euro 2024 da ke gudana yanzu haka a nan Jamus, inda Spaniya za ta fafata da Faransa a wasan farko da ke da zafi matuka.

Euro 2024 | Munich | Allianz Arena | Spaniya | Faransa
Filin wasa na Allianz Arena zai dau haramiHoto: Matthias Koch/picture alliance

Za a gudanar da wannan karawar farko filin wasa na Allianz Arena da ke birnin Munich da karfe tara na daren Talatar wannan mako agogon Jamus, karfe takwas na dare kenan agogon Najeriya da Nijar. Spaniya ta samu nasarar zuwa wannan zagayen ne, bayan ta lallasa mai masaukin baki Jamus da ci biyu da daya. Ita ko Faransa ta samu zuwa wasan ne bayan doke Portugal da ci biyar da uku, a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Mai horas da 'yan wasan Spaniya Luis de la Fuente ya yi fatan ganin Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Turai UEFA ta rushe tsarin karin lokaci wato extra time, a zagayen 'yan 16 da kuma na dab da na kusa da na karshe a gasar ta Euro, domin bai wa 'yan wasa damar buga wasa mai kayatarwa idan an shiga zagayen dab da na karshe wato semi finals da kuma na karshen. A cewarsa hakan zai bai wa 'yan wasan karsashin taka leda ba tare da gajiya ko kasala ba, wadda ya ce karin lokacin na haddasa musu.

Filin wasa na Signal Iduna Park da ke birnin Dortmund na JamusHoto: picture-alliance/Augenklick/firo Sportphoto

Wannan karawa dai kar ta san kar ce domin a shekarar 1984 ma sun hadu da juna a wasan karshe na wannan gasa, inda Faransa ta lashe kofin bayan doke Spaniya da biyu da nema ta hannun Michel Platini da Bruno Bellone. A 1996 kuma suka tashi kunnen doki daya da daya a gasar. A shekarar 2000 kuwa Faransar ce dai ta sake lallasa Spaniya da ci biyu da daya a zagayen dab da na kusa da na karshe. Yayin da Spaniyan kuma ta yi ramuwar gayya a shekarar 2012 a kan Faransar da ci biyu da nema, a zagayen dab da na kusa da na karshe na gasar ta Euro. A daya wasan na Larabar wannan makon, Ingila ce za ta sanya zare da Holland a filin wasa na Signal Iduna Park da ke birnin Dortmund. Ingila ta samu damar zuwa wannan zagaye ne bayan casa Switzerland da ci biyar da uku a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da ita kuma Holland ta doke Turkiyya da ci biyu da daya.