1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a zaben Saliyo

March 6, 2018

Yayin da aski ke zuwa gaban goshi dangane da siyasa a kasar Saliyo, kawunan 'yan siyasa na daukar zafi. A ranar Larabar nan ce ake sa ran al'umar kasar za su kada kuriar zaben shugaban kasa.

Tallar 'yan takara a daya daga cikin titunan Saliyo
Tallar 'yan takara a daya daga cikin titunan birnin Freetown na kasar Saliyo Hoto: DW/Abu-Bakarr Jalloh

Muhimman abubuwan da 'yan adawa ke yakin neman kuri’a da su a zaben na Saliyo, su ne cin hanci da karbar rashawa da suke cewa ya yi kaka gida a kasar. A cewarsu jam’iyya mai mulki ta na bada kwangilar ayyuka a kan kudin da suka zarce hankali. Ita dai jam’iyya mai mulki  All People’s Congress, na takama ne da yadda gwamnatin kasar ta yi kokari na magance cutar Ebola mai saurin kisa, da kuma yadda ta zuba ayyukan raya kasa.

Jam'iyyu goma sha shida ne dai suka tsayar da 'yan takara a zaben shugaban kasr ta Saliyo, kuma galibinsu na kalubalentar gwamnatin da cewa ta gaza farfado da tattalin arzikin ‘yan kasar, inda suka ce sakamakon yadda jam'iyyar APC ta lalata tattalin arzikin kasar. Kashi 70 cikin dari na mutanen kasar na rayuwa ne a kan kasa da dala biyu a rana guda. Amma ita gwamnatin ta hakikance a kan ta yi abin azo a gani. Irin wanann dambarwa ce dai ta sa jama'ar kasar ke ganin a wannan karon, sai sun duba da kyau kafin su kada kuri'arsu.

Hoto: Getty Images/AFP

Zaben na wannan Larabar dai shi ne karo na biyar tun bayan da Saliyo ta fita daga rikicin yakin basasa. Kuma shugaba mai ci yanzu ya yi wa‘adi na biyu. A bisa tsarin mulkin kasar ba zai sake tsayawa takara ba. Mutane sama da milyan uku ake saran za su kada kura'a.