Siriya: Kome cikin dangi bayan shekaru 12
May 19, 2023Ba dai halartar shugaban Siriyan Bashar al-Assad taron kungiyar kasashen Larabawan karon farko cikin shekaru 12 ne kadai ba, shi ma da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi wa taron halartar ba-zata. Babban magatakardar kungiyar ta Larabawa Ahmad Geith ya bayyana cewa, wannnan taron wata dama ce da aka jima ba a samu irinta a tarihin al'ummar Larabawan ba. Shugaba Bashar al-Assad na Siriya da halartarsa taron kungiyar a karon farko cikin shekaru 12 ya fi jan hankali, ya yaba da dawo da kasarsa cikin kungiyar da akayi da kuma alkawarin tallafawa kasar tasa mayar da miliyoyin 'yan gudun hijira da yakin basasar da aka kwashe sheakaru ana gwabzawa ya tilastawa watangaririya a duniya tare da jan hankulan mahalarta taron kan amfani da wannan damar domin samar wa kansu mafita.
Dangane da rikicin Sudan da ya hana shugaban gwamnatin rikon kwaryar sojojin kasar Janar Abdulfattah al-Burhan halartar taron na Jiddah kuwa, wakilin Khartum a taron ya nemi kasashen kungiyar da kar su bayar da kofa ga 'yan tawaye su cimma burinsu na wargaza kasar. A hannu guda shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya kai ziyarar ba-zata azauren taron, domin neman goyan bayan kasashen kungiyar. Galibin kasashen kungiyar ta Arab League na dasawa da Rasha, duk da cewa kasar Siriya ce kadai cikinsu ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga mamayar da Rashan ta yiwa Ukraine din. Saudiyya a nata bangaren ta soki matakin kasashen Yamma na kakaba takunkumai ga Rasha, duk da cewa tana dasawa da su. Karfin ikon da Saudiyya ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya dai, ya yi tasiri a mamayen da Rasha ke yi a Ukraine din.