Assad ya ce a daina tallafawa 'yan ta'adda
September 16, 2014Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ya ce idan har ana so a kaddamar da gangamin yaki da ta'addanci, to ko wajibi ne a sa kaimi kan kasashen da ke goyon bayan kungiyoyin da suka yi dammarar makamai. Kamfanin dillancin labaran kasar na SANA ne ya rawaito shugaban yana cewa yaki da ta'addanci, kamata ya yi a faro shi daga kasashen da suke tallafawa kungiyoyin da suka addabi kasashen Siriya da Iraki suna kuma komawa su zauna su yi kamar ba su ba ne.
Wannan na zuwa ne a yayin da al'ummar kasa da kasa ke yunkurin daukar kwararan matakai kan mayakan IS, wadanda ke da'awar kafa kasar Islama a Siriyar da Irak, inda fadar washington ke kokarin girka hadakar da za ta kunshi kawayenta. To sai dai duk da cewa, Amirka ta ce za ta kai hari ta sama a Siriya, ta ce ba za ta kulla wani kawance da gwamnatin Assad dan cimma burin ta na yakar kungiyar ta IS ba, abin da ya fusata fadar gwamnatin Siriyar da ke Damascus matuka.