1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Assad ya naɗa sabon Firayim Ministan Siriya

August 9, 2012

Wael al-Halqi tsohan ministan kiwan lafiya ya zama sabon Firayim Minista da shugaban Siriya Assad ya naɗa.

The President of the International Committee of the Red Cross, Jakob Kellenberger meets Syrian Health Minister Wael al-Halqi (L) in Damascus April 3, 2012. The Red Cross chief arrived in Damascus on Monday for talks aimed at expanding aid operations and gaining access to all detainees, the agency said. REUTERS/Khaled al-Hariri (SYRIA - Tags: POLITICS HEALTH)
Sabon Fira Ministan Siriya Wael al-Halqi a hannun haguHoto: Reuters

Shugaba Bashar al-Assad na ƙasar Siriya ya naɗa sabon Wael al-Halqi a matsayin sabon Fira Ministan ƙasar, kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar ta bayyana.

Sanarwar ta ce Shugaba Assad ya saka hanu kan ayar doka mai lamba 298, da ta amince da naɗin al-Halqi kan muƙamun na Fira Minista, kuma kafin yanzu shi ne ministan kula da harƙoƙin kula da kiwon lafiya.

Tsohon Fira Ministan ƙasar ta Siriya Riad Hijab ya sauya sheƙa inda ya koma ɓangaren 'yan adawa ranar Litinin da ta gabata. Kuma yanzu haka yana ƙasar Jordan shi da iyalansa.

A wani labarin mayaƙan 'yan tawayen ƙasar ta Siriya, yau Alhamis, sun fice da cikin ɗaukacin yankin Salaheddin na arewacin birnin Aleppo, inda ake ci gaba da bata kashi tsakaninsu da dakarun gwamnati.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu