1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goita: An yi nasarar dakile 'yan ta'adda a Mali

Mouhamadou Awal Balarabe ZMA
April 29, 2026

Kwanaki uku bayan hare-haren kungiyoyin da ke dauke da makamai a Mali, shugaban gwamnatin mulkin soja ya ayyana nasarar shawo kan yanayin tsaro da ya tabarbare.

Russland Moskau 2025 | Assimi Goïta bei Unterzeichnung von Kooperationsabkommen
Hoto: Roman Naumov/Picvario Media/picture alliance

Wannan dai shi ne karon farko da Goïta ya yi jawabi  ga al'ummar Mali tun bayan aika-aika da masu ikirarin jihadi na JNIM da ke kawance da 'yan awaren Azawad na kungiyar FLA suka kai.

Janar Assimi Goïta ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da halin da yake ciki da makomarsa bayan hare-haren da aka kai a birane da dama, inda ya hallara a bainar jama'a bayan kwanaki na gum da bakinsa. Wannan dai ya biyo bayan mawuyacin hali na tsaro da  rashin tabbas da Mali ke fuskanta  bayan hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla fararen hula da sojoji 23, a cewar wani sabon kididdiga da wata majiyar asibiti ta bayar. Amma a jawabin da ya yi ta kafar talabijin, shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali ya ce dakarun kasar sun yi nasarar ja wa 'yan tawaye da masu kishin addini birki.

Karin bayani:Harin 'yan ta'adda ya hallaka ministan tsaron Mali 

" A wannan lokacin da nake magana, an kara tsaurara matakan tsaro, an shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da bincike da tattara bayanan sirri. Ya ku 'yan kasa, yanzu fiye da kowane lokaci,  lokaci ne da za ku dogara kan jami'an tsaro da ke yaki da ta'addanci. Ayyukan soji za su ci gaba har sai an kawar da kungiyoyin da abin ya shafa gaba daya kuma an dawo da tsaro mai dorewa a duk faɗin kasar."

Amma dai Mr. Goïta ya yi karatun ta nitsu game da kalaubalen da Mali ke fuskanta a fannin tsaro da hadin kan kasa, inyd ya danganta da halin da ake ciki da "matsananci". Saboda haka ne ya yi kira ga 'yan Mali da su farka kuma su yi tsayuwar daka wajen yakar rarrabuwar kawuna da neman dare kasa gida biyu.

Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Sai dai shurun da aka fara fuskanta daga bangaren na shugaban Mali ya haifar kace-nace game da makomar mulkinsa, musamman bisa la'akaricda kashe ministan tsaronsa Sadio Camara a hare-hare, da ke zama wani jigo a cikin gwamnatin mulkin soja. Sannan ana yi wa Mr. Camara kallon wanda ya kawo kusanci Mali da Rasha a cikin 'yan shekarun nan bayan da gwamnatin mulkin soja ta kori sojojin Faransa daga Mali a shekarar 2022.

Karin bayani: Shugaban gwamnatin Mali ya bada tabbacin tsaro bayan harin 'yan ta'adda

Hasali ma, Janar Goïta ya gana da jakadan Rasha a Mali Igor Gromyko , inda bangarorin biyu suka tattauna halin da ake ciki a yanzu. Gromyko ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada alkawarin kasarsa ga Mali na ba da gudfunmawa a yaki da ta'addanci," yana mai tabbatar da cewa Rasha za ta ci gaba da zama abokiyar Mali a ko da yaushe.

A cikin wani sako da aka wallafa ta shafukan sada zumunta, ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa 'yan tawaye da masu ikirarin jihadi na sake taruwa kuma Mali na ci gaba da kasancewa cikin mawuyaci. Sannan ma'aikatar ta tabbatar da cewa rundunar sojojin sa kai na Rasha su janye daga birnin Kidal da ke arewaci, wanda masu dauke da makamai suka kwace a karshen makon da ya gabata. Kazalika.

Karin bayani: Sojin Mali da na haya daga Rasha sun fice daga birnin Kidal

Kremlin ta bayyana sha'awar taimakawa wajen dawo da kwanciyar hankali cikin sauri a Mali, wacce ke fama da rikici da tashin hankalin masu ikirain jihadi tun daga 2012.

Kungiyar JNIM da ke da tsaurin ra'ayin addini ta yi barazanar sanya shinge a duk hanyoyin shiga Bamako babban birnin Mali. Amma a cikin wani bidiyo da daya daga cikin masu magana da yawunta ya fitar, ba ta fayyace ko za a aiwatar da wannan yunkuri a cikin 'yan kwanaki masu zuwa ba.

Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Hare-haren da aka kai a ranar Asabar sun jefa shakku kan karfin ikon gwamnatin mulkin soja na dakile barazanar tsaro da kungiyoyi da ke dauke da makamai ke yi ba. Sannan halin da ake ciki ya yi hannun riga da  ikirarin cewa dabarun da ake amfani da su na biyanakudin sabulu bayan raba gari da Faransa da sdauran kasashen yammacin duniya. Amma a daya hannun Janar Assimi Goita ya nuna cewar hadakar kasashen AES da ke Sahel na taimakawa wajen inganta yanayin tsaron Mali.

"A wannan karon, ina yaba wa kokari na hadin gwiwa da aka tsara a kungiyar Kasashen Sahel, wadanda rundunar sojojin hadaka ke aiki ba tare da gajiyawa ba don kawo zaman lafiya a yankinmu. Haka kuma ina so in yaba da ingancin hadin gwiwarmu da abokan huldarmu musamman Tarayyar Rasha."

Karin bayni: Hare-haren 'yan tawayen Mali sun halaka ministan tsaro

A wani mataki da ke nuna alamar rashin kwanciyar hankali a Mali, sojojin gwamnati sun fice daga Gao da ke zama sansannin sojojin na biyu mafi girma baya ga sansanin soja na Kati da ya kasance daya daga cikin wuraren da aka yi fafatawa mai zafi tsakanin sojoji da kungiyoyi masu dauke da makamai. Dangane da birnin Kidal kuwa, yana karkashin ikon 'yan tawaye tun daga karshen mako.  Amma masu sharhi suka ce manufar wannan kawance tsakanin JNIM da FLA ba wai don kwace iko a Bamako ba ne, a'a, sai don sake kwace yankunan arewacin Mali.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani