1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin gaskiya ne ƙasar Kenya ce asulin Barack Obama ?

March 18, 2010

Ko gaskiya ne ƙasar Kenya ce asulin shugaban Amurika Barack Obama?Har yanzu akwai danginsa cen ?

Sarah Obama, kakar Barack Obama zaune a gidanta dake garin Nyangoma ƙasar KenyaHoto: AP

Gaskiya ne, ma´aifin shugaban ƙasar Amurika Barack Obama a ƙasar Kenya aka aife shi, har yanzu iyayen nasa na zaune a Kenya?


Babu shakka tsatson shugaban ƙasar Amurika Barak Obama a ƙasar Kenya yake , domin  kuwa ubansa na wannan ƙasa ne, mussamman ya fito daga wani ɗan ƙauye mai suna Nyangoma dake jihar Nyanza a yammacin ƙasar Kenya.Ma´aifinObama baban jami´i ne a gwamnatin ƙasar Kenya.Ya je kasar Amurika ne da sunan karatu a jami´ar Hawai, inda acen ne ya hadu da wata Mata mai suna Stanley Ann Dunham.Sannu a hankali soyyaya ta shiga tsakanin su har suka yi aure, kuma aure yayi albarka, aka samu aifuwar Barack Obama.

To saidai shi Obama ya baro Amurika ya dawo Kenya, a lokacin da ɗan nasa ya samu shekaru biyu,da aihuwa.Basu sake ganin juna ba sai a shekarar 1971 a yayinda Barak ya samu shekaru goma.

Allah ya karɓi ran Obama a shekara 1982 a cikin wani haɗarin mota  a ƙasar Kenya.

Amma har yanzu akwai kakarsa mai suna Sarah Hussein Onyango Obama,mai shekaru kusan 90 a duniya, ta na nan da ranta daram a Kenya, tana zaune a ƙauyen Nyangoma, da sauran iyaye,  ƙannai da dangin shugaban ƙasar Amurika Barak Obama.

To shi Obama ya taba zuwa Kenya kuwa ?

Sau daya rak Barak Obama yaje kasar Kenya domin ya ga asulinsa ya kuma gana da danginsa.ya isa har garin ma´aifansa wato Nyangoma a watan Ogusta na shekara 2006.A lokacin ´yan jarida suka yiwa garin acam!!!


Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Ahmed Tijani Lawal