1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asusun IMF na ƙara matsa ƙaimi kan babban bankin Turai

September 25, 2011

An nuna damwua game da yaɗuwar matsalolin bashi a nahiyar Turai zuwa Amirka da sauran ƙasashen duniya.

Christine Lagarde daraktar assusn IMFHoto: dapd

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi kira ga babban bankin Turai da ya ƙara taka muhimmiyar rawa wajen gano bakin zaren warware matsalolin bashi a Turai. Bisa kalaman shugaban ɓagaren asusun na IMF a nahiyar Turai, Antonio Borges, babban bankin Turai ne kaɗai zai iya fid da tsoro daga kasuwannin hada hadar kuɗi. Har yanzu dai ana ci-gaba da duba hanyoyin magance matsalolin rikicin kuɗin. A taron Bankin Duniya da asusun IMF na wannan rubu'in da aka kammala a wannan Lahadi, an fi mayar da hankali kan damuwar da ake nunawa game da yiwuwar bazuwar matsalolin baussukan da suka yi wa ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro katutu, zuwa Amirka da ƙasashe masu tasowa da kuma ƙasashe masu samun bunƙasar tattalin. Shugaban Bankin Duniya Robert Zoellick da sabuwar babbar daraktar IMF Christine Lagarde sun yi kira ga ƙasashe masu arzikin masana'antu da su ɗauki nagartattun matakai bisa wannan munafa da aka sa gaba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman