1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asusun IMF ya yaba da matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Jamus

Mohammad Nasiru AwalNovember 8, 2003

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya yaba da matakan farfado da tattali arziki da gwamnatin tarayyar Jamus ke dauka. Asusun na IMF ya ce matakan da gwamnatin Jamus ta ke aiwatarwa musamman dangane da garambawul da take yiwa manufofin kiwon lafiya, fansho da kuma kasuwar kwadago zasu taimaka wajen samun bunkasar tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa. A cikin wani rahoto da ta fitar, hukumar zartaswa ta asusun IMF ta yi hasashen cewa a cikin shekara mai zuwa Jamus zata samu bunkasar kashi 1.5 cikin 100, duk da koma bayan tattalin arziki da aka samu cikin wannan shekara. Asusun IMF ya ce karfin darajar takardun kudi na Euro da rashin ciniki na kayan da ake fitarwa ketare musamman a kasashen kungiyar tarayyar Turai EU da kuma gibin kasafin kudi na daga cikin dalilan da suka janyo koma-bayan tattalin arziki. A dangane da haka wasu daraktocin IMF sun ba da shawara da a kara rage haraji, muddin tattalin arzikin Jamus bai farfado kamar yadda aka yi zato ba. Bugu da kari asusun na IMF ya ce ko da yake shirin aiwatar da canje-canjen a fannin haraji a shekara ta 2004 maimakon ta 2005 zai yi kyakkyawan tasiri wajen farfado da tattalin arziki, amma dole sai an ci-gaba da daukar sahihan matakai bisa manufar ta da komadar tattalin arzikin wannan kasa. Hakan kuwa ya hada da aiki da shirin nan na ajanda ta 2010 wanda ya tanadin yin canje canje a tsarin kiwon lafiya da fansho sai kuma matakan tsuke baki aljihun gwamnati. Wasu daraktocin asusun na IMF sun nuna damuwa kan cewa bisa ga dukkan alamu Jamus ba zata iya kauracewa samun gibin kasafin kudi na kashi 3 cikin 100 a badi ba. To sai dai masana na harkaokin tattalin arziki sun imani cewa da gaske ministan kudin Jamus yake wajen gaggauta daukar matakan rage kashe kudi don cimma manufar da aka sa a gaba.