SiyasaJamus
Asusun IMF ya yafe wa kasashen Afirka bashi
October 8, 2021Talla
Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya fitar da sunayen wasu kasashe matalauta 24 wadanda zai yafe wa basukan da yake bin su, domin ba su damar warware matsalolin da suka shiga saboda corona.
IMF ya ce basukan da yake yafewa a karo na hudu saboda coronar, sun kai na miliyan 973 na dala, kari kan miliyan 124 da ya yi tun da fari.
Kasashen dai sun hada har da wadanda suka ranto kudade a baya-bayan nan wato Lesotho da Kyrgystan.
Wasu kasashen sun hada da Benin da Burkina Faso da Mali da Nijar da kasashen Guinea Conakry da Guinea Bissau da Tsibirin Comoros.
Haka ma akwai kasashe irin su Gambiya da Burundi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Habasha da Laberiya da Haiti da kasar Malawi.