ADC ta yi martanin hukuncin dakile takarar Atiku
November 5, 2026
Hankula dai a tashe suke a tsakanin yayan jamiyyar ADC da shugabaninsu, musamman wandana suka samu takara bayan wannan hukuncin da babbar kotun ta yanke a Abuja. Sakiya ce da babu ruwa aka yiwa jamiyyar ta ADC bisa abinda mai shari'a Peter Lifu ya gabatar na haramta shugabancin Sanata David Mark na jamiyyar ta ADC, abin da ya shafiu daukacin yan takarar jamiyyar, abinda hukuncin ke nufi shi ne a yanzu jamiyyar ba ta da ‘yan takara a zaben da za a yi.
Abin da 'yan adawa ke cewa
A cikin fushi jamiyyar ta da sanarwa tana gargadin cewa a yi taka tsantsan a kan hukuncin. Hon Maigari Bello Kasimu dan kwamitin zartaswa ne na jamiyyar ADC a Najeriya, wanda ya ce wannan hukuncin bai zo da bazata ba.
A yayin da ADC ke ci gaba da taro don neman mafita a kan wannan hali da suka tsinci kansu a ciki, sao'I 24 bayan kadammar da yakin neman zaben jamiyyar. Tuni Hon Nafi'u Bala Gombe da ya kwashe shekaru biyu yana wannan sha'ria ya shiga murna a kan abinda ya kira samu karbar ragamar jamiyyar ta ADC.
Jamiyyun adawar Najeriya sun dade da kara cewa ana hanasu sakat a yakin neman zaben da suke yi. Omoyele Sowere shi ne dan takarar neman shugaban Najeriya na jamiyyar African Action Congress AAC, inda ya ce manufar wannan shi ne a hana jam'iyyun siyasa mayar da hankali a yakin neman zabe domin ana saura watani uku a yi zabe ne wannan ke faruwa.
Ko yaya masana kimiyyar siyasa ke auna fagen siyasar Najeriya bisa la'kari da halin da ake ciki? Dr Abdurrahman Abu Hamisu masanin kimiyyar siyasa ne da ke Abuja.
Kodayake bangaren Sanata David Mark na jamiyyar na shirin daukaka kara, amma akwai tsoron lokaci na kara kure masu saboda an jefa magoya bayansu cikin hali na rashin tabbas.