1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku: Sai mun tabbatar da gaskiya a kotun koli

Uwais Abubakar Idris
October 5, 2023

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce zargin takardun boge da jam'iyyarsa ke yi wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu batu ne na kare mutuncin Najeriya don haka babu gudu babu ja da baya

Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Wannan ne karon farko da dan takarar neman shugabancin Najeriyar Atiku Abubakar ya maida martani a kan zargin gabatar da takardun bogen da yake yi wa shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, batun da shine babban lamarin da ya dage a kansa a kalubalantar zaben da yake yi a kotun koli. Atiku Abubakara da wannan  ne karon farko da ya yi bayani tun bayan da jamia'ar Chicago ta Amurka ta fitar da takardun nasa. Tsohon mataimakaion shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya bayyana cewa.

Najeriya I Atiku AbubakarHoto: Afolabi Sotunde/File Photo/File Photo/REUTERS

Ya ce tsarin Mulki ya shimfida kaida na takardun ga duk wadanda za su nemi shuigabanci, don haka bai kamata a dauki watanni kafin tabbatar da sahihancinsu ba, dole ne a yi aiki da dokokin da aka tsara na mulki a kasarmu, domin mutuncin kasarmu shine a gaba kuma wannan ya shafi dukkanin ‘yan Najeriya ko a ina suke, don haka ba zan ja baya ba har sai kotu ta yanke hukunci''

Karin Bayani: An fara kalubalantar Bola Tinubu a Najeriya

Amma me ke kunshe a cikin takardun da jami'ar ta bai wa lauyoyin Atiku da suke jin suna da kwarin gwiwa a kai. Barrister Kalu Kalu na cikin lauyoyin Atiku.

Najeriya I Atiku AbubakarHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

‘'Ya ce na farko Bola Ahmed Tinubu ya bayar da jabbun takardun da ya aika wa hukumar zabe, na biyu sunan da ke a takardar kammala makaranta ya nuna mace ce, na uku takardun sun nuna cewa Bola Ahmed Tinubu na da takardun sakandare da ya nuna ya kammala sakandare a 1970 bayan kuwa a Zahiri an kafa makarantar ce a 1974, sannan takardar shaidar yi wa kasa hidima da ya bayar na da suna Bola Adekunle bayan kuwa, ban san inda Adekunle ya hadu da Ahmed ba''

Karin Baya:Matsaloli kan zaben Najeriya

Tuni dai bangaren gwamnatin Najeriya ya maida martani a kan wannan batu bisa cewa jam'iyyar PDP da dan takararta suna bata lokaci ne kawai. AbdulAziz AbdulAzi daya ne daga cikin masu taimaka wa shugaban a fanin yada labaru.

Kotun kolin Najeriyar dai ta tsayar da ranar 15 ga watan Disdamba domin yanke hukunci a wannan shari'a da ke daukar hankali a Najeriyar