1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku zai tsaya takara a zaben 2015

Ubale MusaSeptember 24, 2014

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya baiyyana aniyarsa ta neman kujerar shugabancin Najeriyar a zaben shekarar 2015.

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015 Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Team

A wani bikin da ya samu halartar dubun dubatar magoya bayansa a Abuja, Alhaji Atiku Abubakar da yake takarar karkashin inuwar jam'iyyar APC ta adawa ya ce kasar tana matukar bukatar ceto daga barazanar rushewa da rashin iya shugabanci ya haifar cikin dan kankanen lokaci.

Ana sa ran takara mai zafi a tsakanin Atikun da tsohon shugaban kasar Janar Muhammad Buhari da kuma gwamnan jihar kano Rabi'u Musa Kwankwaso a gwagwarmayar neman tikitin jam'iyyar ta APC da ke kara farin jini a sassa daban daban na kasar.

Barazanar rushewa saboda rashin iya shugabanci

Atiku da ya ce ya zo ne "domin ceton kasar daga halin rashin tsaro da ma rashin iya mulki" inda ya ce sauyi na zaman wajibi ga kasar da ke burin kaiwa ga tudun mun tsira.

"Ba zai yiwu mu ci gaba bisa turbar rushewar da muke yanzu haka ba, ba zai yiwu mu dore a cikin bakin ciki da bacin ran da muke gani a halin yanzu ba. Kasarmu na rabe a yanzu fiye da kowane lokaci bayan yakin basasa. Ga kuma karuwar kururuwar kabilanci da kuma ihun addini abun da ke jawo dardar da tada hankalin al'umma. 'Yan fashi da makamai na cin karensu babu babbaka. Sannan kuma wasu can 'yan iska na daga wata bakuwar tuta a cikin filin kasarmu mai fadin da suke ikirarin kamawa. Abun da muke fuskanta yanzu shi ne gazawa na gwamnati, kai in muku 'yar kururu muna cikin jirgin da babu matuki kansa."

Muhammadu Buhari da Atiku AbubakarHoto: Atiku Media Office

To sai dai koma ta ina Atikun yake shirin tunkarar jerin matsalolin dai, kwarewar mulkin Atiku dai na zaman babban makamin da ke iya taimaka wa 'yan kasar ga samun sauyin da suke nema a fadar Ambasada Yahaya Kwande, jigo a jam'iyyar APC.

"Na rantse da Allah a yau dai a cikin wadanda ke filin nema babu wanda gwamnatin ke tsoro kamar Atiku, har abubuwan da ke hannunsu har jama'ar da ke musu banbado. In dai ana bukatar canji to lokaci ya zo na tabbatar da samun canjin."

Atiku a matsayin mai ceto?

Sauyi dole ko kafar katako ko kuma kokari na samun mulki dai, a fadar senata Aisha Alhassan da ke zaman yar jam'iyyar a jihar Taraba, bullar Atikun na zaman sako daga mahallicin da ke bukatar tausaya bayinsa da ke cikin ukubar PDP

“Mutane sun gaji ne da shugabancin PDP domin mutane suna shan wahala, saboda haka muna ganin Allah zai bashi saboda yana son ragewa 'yan Najeriya wahala”

Dan aike ko kuma mai neman tara abun hannunsa dai a baya ana zargin Atikun da zama daya a cikin masu ruwa da tsaki da rusa cigaban tattalin arzikin kasar zuwa aljihunsa.

Atiku a tsakiyar magoya bayansaHoto: DW/U. Musa

Abun da a cewar tsohon maigidansa Chief Olusegun Obasanjo ya kaisu ga takun saka na lokaci mai nisa.

To sai a fadar Senata Bindo Jibrila da ke wa jihar Adamawa takara ta gwamna na jihar, Atiku na zaman bango na gabas ga demokaradiyyar kasar ta Najeriya a halin yanzu.

“Kai kasan yadda Atiku ya yi fada da Obasanjo kan zancen zarcewarsa, in da ba dan Atiku ba da yanzu babu ma demokaradiyyar da muke yi. Shi ya gyara tafiyar da muke yi, baya cikin wadanda suka bata kasar nan.”

Abun jira a gani dai na zaman nisan ruwan na Atiku da majiyoyi suka ce tuni ya kai ga mallakar jiragen yakin neman zabe.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani