1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku zai yi wa jam'iyyar PDP takara

October 7, 2018

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta zabi Atiku Abubakar a matsayin wanda zai yi mata takara a babban zaben kasar.

Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a babban zaben kasa a badi.

Atiku dai ta tabbata shi ne zai fafata da shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda shi ma jam'iyyarsa ta APC ta tabbatar a zaben da ta yi a ranar Asabar.

A sakonsa ta shafin twitter, Atiku ya ce nasarar ta sa, ta mikewa tsaye ne don kyautata makomar Najeriya.

Ya kuma gode wa tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, da taimakon da ya bayar har ya kai ga samun nasarar.

Babban batun da ke gaban 'yan takaran shi ne matsalar tattalin arzikin da kasar ke ciki, kasar da ta fi kowacce karfin arziki a nahiyar Afirka.