1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Atisayen Rasha da Belarus ya tayar da hankali kasashen Yamma

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2025

Hukumomin Moscow da Minsk sun yi amfani da sojoji da motoci masu sulke da sauran makamai wajen nuna karfin kayan yakinsu, bayan kutsen da jiragen Rasha suka yi a Poland, lamarin da ya haifar da fargaba a kasashen NATO.

Belarus da Rasha sun yi wa atisayen sojoji da kayan yakinsu lakabi da Zapad 2025
Belarus da Rasha sun yi wa atisayen sojoji da kayan yakinsu lakabi da Zapad 2025Hoto: Russian Defense Ministry Press Service/AP Photo/picture alliance

Rasha da kawarta Belarus sun fara wani atisayen soji na hadin gwiwa wanda ya kunshi dubban sojoji da motoci masu sulke da jirage masu saukar ungulu, matakin da ya haifar da damuwa a kasashen yammacin duniya, kwanaki kalilan bayan kutsen da jiragen Moscow marasa matuka suka yi a kasar Poland.

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da sojojin Rasha ke ci gaba da kai hare-hare ta sama kan garuruwan Ukraine, duk kuwa da yunkurin diflomasiyya na kawo karshen hare-haren da aka kwashe shekaru uku da rabi ana yi.

Karin bayani: Kokarin Turai na kawo karshen yakin Ukraine

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce wannan atisayen ya kunshi ayyukan kandagarkin soji domin shirya martani a kan iyakokinta idan abokan gaba suka kai musu hari.

Sai dai kasashen Poland, Lithuaniya da Latviya da ke makwabtaka da Belarus, sun yi tir da wannan atisaye, inda suka ce za su gudanar da nasu atisayen soji a cikin kwanaki masu zuwa a matsayin martani.