1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atisayen sojin Rasha da China

Usman ShehuApril 23, 2012

Ƙasashen Rasha da China sun fara atisaye mafi girma kana na farko tsakanin rundanar sojin ƙasashen biyu

In this photo released by China's Xinhua News Agency, Rear Adm. Du Xiping, front right, deputy commander of China's Beihai Fleet, shakes hands with Captain First Rank Sergei Yuriyevich Zhuga of Russia's Pacific Fleet during a welcome ceremony at a naval base in Qingdao, east China's Shandong Province, Saturday, April 21, 2012. A China-Russia joint maritime drill is scheduled from April 22 to 27 on the Yellow Sea, Xinhua said. (Foto:Xinhua, Zha Chunming/AP/dapd) NO SALES
Hafsoshin sojin ruwan Rasha da ChinaHoto: dapd

Ƙasashen China da Rasha sun fara atisayen haɗin gwiwa na sojojin ruwan su a wannan Lahadin. A cewar kanfanin dillancin labaran ƙasar China, atisayen, wanda ke zama irin sa na farko, za'a ɗauki tsawon kwanaki shidda ne ana yin sa akan tekun dake gabashin China na Yellow Sea. China ta tura manyan jiragen ruwan ɗaukar ƙananan jiragen saman yaƙi guda biyu, kana da manyan jiragen ruwa 16 da kuma fiye da sojoji dubu huɗu, a yayin da Rasha kuma manyan jiragen ruwa bakwai da suka haɗa da waɗanda ke lalata makamai masu lnzami. Atisayen soji na ƙarshen da ƙasashen biyu suka yi haɗin gwiwar yin sa dai ya kasance a shekara ta 2005 ne, amma kuma wannan shi ne atisaye na farkon daya shafi mayaƙan ruwa, kamar yanda wani ƙwararre a ƙasar China ya sanar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas