1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU na fargabar barkewar annobar kyandar biri a Afirka

October 31, 2024

AU ta bayyana fargaba a game da yiwuwar rikidewar cutar kyandar biri (Mpox) zuwa annoba a Afirka bayan da cutar ta yi ajalin fiye da mutane 1,000 daga cikin mutane kusan 48,000 da suka kamu da ita.

AU na fargabar barkewar annobar Mpox a Afirka
AU na fargabar barkewar annobar Mpox a AfirkaHoto: Fareed Khan/AP Photo/picture alliance

Hukumar lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadi a Alhamis din nan kan cewa har kawo wannan lokaci ba a shawo kan cutar kyandar biri da ake wa lakabi da Mpox ba, tare kuma da kiran kasashen kungiyar da su hada kai don guje wa barkewar gagarumar annoba da ta fi Covid-19 muni.

Kawo yanzu dai cutar ta Mpox ta yi ajalin fiye da mutane 1,000 a Afirka a cikin mutane kusan 48,000 da suka kamu da ita, kamar yadda alkaluman da cibiyar rigakafin cutuka masu yaduwa ta nahiyar suka nunar. Galibin mace-macen da cutar ta haddasa sun auku ne a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango inda cutar ta fi kamari duk da matakin yin allurar rigakafi da mahukuntan kasar suka dauka a farkon wannan wata. 

Karin bayani:Jamus na taimaka wa Kwango gano masu fama da kyandar biri 

Kungiyar ta Tarayyar Afirka ta ce lamarin ya fara zama abin damuwa a kasar Yuganda inda aka ba da rohoton mutuwar mutum na farko da ya kamu da cutar ,yayin da adadin sabin kamuwa ya karu zuwa mutane 830.