AU na son a tsaurara tsaro a Burundi
May 21, 2016Talla
Masu bincike na kungiyar tarayyar Afirka AU kan hakkin dan Adam suka ce akwai bukatar da ke akwai ta ganin an tura jami'an 'yan sanda na kasa da kasa zuwa kasar ta Burundi baya ga wasu jami'an da AU din ta rigaya ta tura.
AU din ta ce 'yan sanda za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kiyaye rayukan mutane musamman ma a wuraren da suka yi kaurin suna yanzu haka wajen fuskantar tashin hankali.
Wannan butaka ta kungiyar ta AU dai na zuwa ne gabannin hawa teburin sulhu da za a yi kan rikicin kasar ta Burundi a birnin Arusha na Tanzaniya sai dai rahotanni na cewar za a yi zaman ne ba tare da wakilan 'yan adawa ba.