1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tarayyar Afirka tana son sojoji su bar mulkin Chadi

April 24, 2021

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta yi kira da a yi hanzarin dawo da mulkin farar hula a kasar Chadi.

Äthiopien Eröffnung des Gipfeltreffens der Afrikanischen Union in Addis Abeba | Moussa Faki Mahamat
Hoto: Giscard Kusema/Press Office Presidency of DRC

Shugaban kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar ta AU kuma Tsohon Firaministan Chadi Moussa Faki Mahamat ya nuna damuwa a kan dakatar da tsarin mulkin kasar da rusa majalisar kasar da sojojin Chadin suka yi, yana mai kira ga sojojin da su kama aikin dawo da kasar tafarkin dimukuradiyya.


Tun dai a ranar Alhamis kungiyar ta  Tarayyar Afirkan ta tattauna wannan matsaya amma ta dakatar da fitar da sanarwa har sai bayan jana'izar marigayi shugaba Idriss Deby da aka yi a ranar Jumma'a. 


Kungiyar ta AU ta ce za ta tura tawaga ta musamman zuwa Chadi don duba halin da ake ciki, tana mai bukatar sojojin da su kaddamar da tsarin tattaunawa da bangarorin siyasa na kasar don samar da mafita. 


Wannan dai na zuwa ne a yayin da a gefe guda kungiyar 'yan tawayen FACT wace a wurin arangama da ita ne sojojin Chadi suka ce marigayi Idriss ya samu raunin  da ya zama ajalinsa, ta lashi takobin ci gaba da kokarin ganin ta kwace iko da kasar bayan tsagaita wutar da ta yi a jiya Jumma'a don a yi jana'izar idriss Deby cikin lumana. Sai dai kungiyar AU ta yi gargadin lamarin ka iya shafar sauran kasashen Afirka.