1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU ta bukaci jin bahasin mutuwar 'yan ci-ranin Afirka

June 28, 2022

Kungiyar AU ta yi kira da a kaddamar da bincike tare da tunasar da kasashe kan mutunta 'yan ci-rani kamar yadda dokoki suka yi tanadin hana amfani da karfi a kan 'yan ci-ranin.

Symbolbild African Union | Mahamat Moussa Faki
Hoto: John Thys/AFP

Shugaban hukumar gudanarwa ta Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, Moussa Faki Mahamat ya nuna bacin ransa a game da rahotan mutuwar 'yan ci-ranin Afirka 23 da ake zargin an gallaza wa azaba kafin mutuwarsu a kokarin da suka yi na shiga kasar Spain daga Moroko.
A ranar Jumma'a ce dai aka yi artabu a tsakanin 'yan ci rani wurin 2,000 da suka yi yunkurin tsallakawa Spain daga iyakar Moroko da kuma jami'an tsaro, lamarin da ya haifar da tashin hankalin da ya yi ajalin mutum 23.