1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU ta ja hankalin Habasha da Somaliya

Abdullahi Tanko Bala
January 4, 2024

Kungiyar tarayyar Afirka ta bi sahun Amurka wajen kiran kwantar da hankula da kuma kai zuciya nesa bayan tsamin dangantakar da ta biyo bayan wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin Habasha da yankin Somaliland

Zauren taron kungiyar tarayyar Afirka
Zauren taron kungiyar tarayyar AfirkaHoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Wondimu Hailu

Kasar Somaliya dai ta ci alwashin kare yankinta bayan yarjejeniyar wadda ta baiyana a matsayin cin fuska da kuma tsokanar fada kan iyakokinta daga makwabciyarta kasar Habasha.

Karin Bayani: Rikici na ci gaba a yankin Somaliland

Shugaban hukumar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat a cikin wata sanarwa ya yi kiran nuna halin dattako da mutunta juna tsakanin Habasha da Somaliya.

Ya kuma yi kiran kasashen biyu su fara tattaunawa ba tare da jinkiri ba don warware takaddamar cikin lumana

Faki ya kuma bukaci su kauce wa dukkan wani abu da zai iya kai wa ga bata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin makwabtan kasashen biyu na gabashin Afirka.