1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta jinjinawa Burkina Faso

Ahmed SalisuNovember 18, 2014

Ƙungyiar kasashen Afrika ta AU ta jiniwa Burkina Faso dangane da warware rikicin siyasar ƙasar da ya kunno kai bayan murabus ɗin tsohon shugaban ƙasar Blaise Campaore.

Michel Kafando Übergangspräsident Burkina Faso 17.11.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Frank Franklin II

AU ɗin ta ce ta kuma jingine dukanni wani shiri da ta ke na maida Burkina Faso ɗin saniyar ware a tsakanin ƙasashen ƙungiyar tunda dai masu ruwa da tsaki a ƙasar sun kai ga tabbatar da farar hula da zai riƙe madafun iko a matsayi na rikon kwarya.

Shugaban riƙon ƙwaryar dai Michel Kafando wanda tsohon jami'in diflomasiyya ne ya sha rantsuwar kama aiki a Talatar nan inda ya lashi takobin ɗorewar tsarin mulkin farar hula a ƙasar.

A gobe Laraba nan ce ma ake sa ran zai bayyana sunan firaministan da zai yi aiki tare da shi wanda za su hada gwiwa wajen fidda mutane 25 da za su yi aiki a majalisar ministocin ƙasar.