1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta yaba da zaɓen Sudan

April 14, 2010

Ƙungiyar AU ta baiyana farin ciki da zaɓen sudan cewa yana gudana cikin kwanciyar hankali.

Shugaba Omar al-Bashir na ƙasar Sudan.Hoto: AP

Ƙungiyar gamaiyar Afirka ta yaba da yadda ake gudanar da zaɓɓuka a ƙasar Sudan tana mai cewa  baá sami tarzoma da tashe tashen hankula ba duk da matsalolin da aka fuskanta na kayan aiki da kuma sufuri. Masu lura da alámuran yau da kullum na ganin cewa zaɓɓukan na gudana ba tare da wasu manyan matsaloli ba. Shugaban hukumar gamaiyar Afirka Jean Ping ya shaidawa manema labaru a birnin Addis Ababa cewa baá sami wani rahoton tashin hankali ba. A ranar lahadin da ta wuce ne dai aka fara gudanar da zaɓen na gama gari a Sudan wanda shine irinsa na farko bisa tafarkin Jamíyu da dama a shekaru kusan 24 da suka gabata. Ana kyautata tsammanin shugaba Omar al Bashir zai lashe zaɓen sakamakon janyewar wasu manyan yan takara.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

 Edita: Umaru Aliyu