AU ta yi Allah Wadai da harin Somaliya
February 29, 2016Talla
Birnin dai na Baidoa wanda ke samun kulawar dakarun hadaka na rundunar Tarayyar Afrika kimanin dubu 22 mai suna AMISOM ya fuskani harin kungiyar ta al-Shabbab ne a ranar lahadi nan. A inda mutane kimamin 30 suka hallaka a yayin da wasu 61 suka samu raunuka daban-daban.
A nasa bangaren gwamnan birnin Abdurashid Abdullahi ya ce, daga cikin wadanda suka sami raunuka, 15 suna nan cikin mawuyacin hali a inda ya kara da cewar harin ya faru akan cikin tsakiyar wani wajen hada-hadar harkoki ciki da mutane a birnin na Baidoa.
Tuni dai kungiyar ta Al-shabbab ta yi ikirarin cewar itace ke da alhakin harin na Somaliya.