AU ta yi maraba da kwance wa 'yanbindiga damara a CAR
July 18, 2025
Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yi maraba da kwance wa wasu manyan kungiyoyin 'yanbindiga guda biyu damara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A sanarwar da ta fitar ranar Juma'a, AU ta kuma yi kira ga sauran masu dauke da makamai da su ajiye makamansu.
Halin kunci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Jamhuriyar CAR na daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, kuma ta sha fama da jerin yake-yaken basasa da kuma mulkin kama-karya tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960.
Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a 2019 tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyi 'yantawaye guda 14, har yanzu wasu kungiyoyi dauke da makamai na ci gaba da fada da ikirarin iko da wasu sassan kasar.
MDD ta ce yakin Sudan zai iya shiga Afirka ta Tsakiya
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a kafafen sada zumunta, Shugaban AU, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi maraba da matakin ajiye makamai da kungiyoyin da suka hada da UPC da 3R, suka yi kamar yadda shugabanninsu suka sanar a ranar 10 ga watan Yulin 2025.