1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulki a Afirka: AU ta magantu

Abdullahi Tanko Bala LMJ
February 7, 2022

Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU sun yi kakkausar suka kan jerin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan a wasu kasashen nahiyar, wanda ya janyo kungiyar da dakatar da su daga wakilci a cikinta.

Habasha | Taron AU a Addis Abeba
Shugaban kasar Senegal, kana asabon shugaban kungiyar AU Macky SallHoto: Tony Karumba/Getty Images/AFP

A karshen taron koli karo na 35 da suka kammala ne dai, kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yi sukan. Batun yawaitar juyin mulki a nahiyar ta Afirka dai, na daga cikin muhimman batutuwan da taron shugabannin ya mayar da hankali a kai. Da yake bayani ga 'yan jarida kan jawabin bayan taron, shugaban majalisar tsaro da zaman lafiya na kungiyar ta AU Bankole Adeoye ya ce daukacin shugabannin sun yi tir da haramtattun juye-juyen mulkin da sojoji suka yi. Kasa da makonni biyu gabanin taron dai, Burkina Faso ta zama kasa ta hudu da kungiyar ta Tarayyar Afirka ta dakatar bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Roch Marc Kabore. 

Karin Bayani: Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali

Tuni dama dai kungiyar ta AU ta dakatar da kasashen Guinea da Mali da kuma Sudan. Sai dai kuma yayin da kungiyar ta AU ke cewa ta dauki matakin dakatarwar domin ladabtar da jagororin juyin mulkin, masana na cewa kamata ya yi kungiyar ta kara himmantuwa wajen hana juyin mulkin. An kuma zargi kungiyar ta AU da rashin zama kaifi daya, musamman da ta ki dakatar da kasar Chadi yayin da sojoji suka karbe ragamar mulki bayan rasuwar Shugaba Idris Deby Itno a watan Afrilun bara.
Taron shugabannin ya kuma tattauna kan bukatar Afirka na samun wakilcin kujerar din-din-din a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda firaministan Habasha Abiy Ahmed ya yi tsokaci yana mai cewa: "Lokaci ya yi na yi wa Majalisar Dinkin Duniya kwaskwarima da kuma yi mata kaimi domin dacewa da yanayin da ake ciki yanzu a duniya, a kuma tabbatar da karin wakilcin kasashe. Bisa ga kudirin da muka dauka a taronmu na Ezulwini a 2005, ya kamata mu dage kan cewa Afirka na bukatar kimanin kujeru biyu na din-din-din da kuma wakilcin da ba na din-din-din ba guda biyar, a Kwamitin na Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar."

Zauren taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU karo na 33Hoto: Shadi Hatem/APA Images/ZUMAPRESS/picture alliance

Karin Bayani: Juyin mulkin soja ya gagara a Guinea Bisau

Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi wanda ya kammala wa'adin shekara guda na jagorancin kungiyar ta Afirka, ya bukaci hada karfi da karfe domin cimma manufar da kungiyar ta sanya a gaba. Taron dai ya zabi shugaban kasar Senegal Macky Sall a matsayin sabon shugaba, domin maye gurbin Felix Tshisekedi wanda ya kammala wa'adin jagorancinsa na kungiyar ta AU. Sabon shugaban wato Macky Sall ya yi waiwayen baya, inda ya yaba da gudnmawar da shugabbanin suka bayar na tabbatar da wanzuwar kungiyar hadin kan Afirka. Taken taron na bana dai shi nez, jajircewa wajen samar da wadatar abinci mai gina jiki a Afirka da bukasa rayuwar al'umma da inganta jin dadi da walwarsu da kuma bunkasa tattalin arziki.