1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsayar AU a taron kan sauyin yanayi

September 6, 2023

Shugabanni kasashen Afrika sun yi alkawarin samar da dala biliyan 23 wajen inganta hanyoyin samar da tsaftataccen makamashi domin fuskantar matsalar sauyin yanayi.

AU za ta samar da dala biliyan 26 domin yaki da sauyin yanayiHoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Yayin da ake shirin karkare taron kolin na kwanaki uku kan sauyin yanayi karo na farko da shugannin kasashen Afrika suka shirya a kasar Kenya, shugaban kasar Kenya mai masauki baki Willian Rutu ya ce ko baya ga nahiyar Afrika matakan da suka yanke shawarar dauka za iya tasiri a duniya baki daya domin bullo wa lamarin sauyin yanayi da ke da ke haddasa ibtila'o'i ciki har da ambaliyada kuma fari.

Karin bayani: Kasashen Afrika na taro kan sauyin yanayi

A mairaincan nan wannan Laraba (06.09.2023) shugabannin kasashen za su fitar da sanarwar bai daya wace za su gabatar a taron koli na duniya kan sauyin yanayi na COP28 wanda za a gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa a karshen watan Nowamba mai zuwa.

Karin bayani: Illar sauyin yanayi a Afirka

A cikin sanarwar ana sa ran shugabannin za su bukaci kasashe masu karfin masana'antu da su duba yiwuwar yafe wa kasashen Afrika basusuka a matsayin diyyar dumamar yanayin da suke haddasawa.

Karin bayani: Bukatar yafe bashi ga Najeriya da kasashe matalauta