1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Australiya ta hana yara amfani da shafukan sada zumunta

December 10, 2025

Firanministan Australiya, Anthony Albanes ya yi maraba da doka ta farko a duniya, da za ta haramta wa yara 'yan kasa da shekaru 16 amfani da kafafen sada zumunta.

Australiya ta hana yara amfani da shafukan sada zumunta
Hoto: Matthias Balk/dpa/picture alliance

A cewar firanministan Australiya, Anthony Albanes, dokar da za ta fara aiki a wannan Larabar a kasar, za ta ba wa iyaye damar sa ido tare da kare yaransu daga wadannan kafofi, sai dai za a sha wahala wajen aiwatarwa.

Karin bayani: Najeriya: Rufe kafofin sada zumunta ne mafita?

Wasu iyayen sun ce yaransu sun fusata bayan da suka gano an rufe musu shafukansu na sada zumunta. Iyaye da dama ne a kasar ta Australiya suka nuna farin cikinsu ga sabuwar dokar, musamman iyayen da yaransu suka kashe kansu a dalilin wadannan kafofin. Dokar ta kuma tanadi hukuncin biyan tara na kimanin dala miliyan 33 kan kamfanoni irinsu Facebook da Instagram da TikTok da Snapchat da X, idan ba su dotse shafukan yaran 'yan kasa da shekaru 16 ba.

Kwamishiniyar da ke sa ido kan internet a kasar, Julie Inman Grant ta ce kawo yanzu an rufe shafukan TikTok na yara fiye da dubu 200 a kasar.