1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Austria za ta tilasta yin rigakafin corona

Abdullahi Tanko Bala
November 19, 2021

Austria ta zama kasa ta farko a nahiyar Turai da ta sanar da tilasta yin allurar rigakafin corona kuma daga mako mai zuwa za ta sanya kwarya-kwaryar dokar kulle sakamakon cutar corona da ke cigaba da yaduwa.

BG Europaweiter Kampf gegen Covid-19
Hoto: Lisi Niesner/REUTERS

Dokar kullen wadda za ta fara aiki daga ranar Litinin ta na daga cikin tsauraran matakai da aka sake bullo da su a nahiyar Turai a 'yan  makonnin nan ganin yadda cutar ke yaduwa a fadin nahiyar saboda yadda wasu ke kin karbar allurar rigakafin.

A karkashin dokar kullen ta kwanaki 20 ba za a bar mutane su fita ba sai dai zuwa wurin aiki ko kanti domin sayin kayan amfanin gida da suka zama wajibi.

Sai dai kuma ba za a rufe makarantu ba duk da cewa an umarci iyaye su kula da 'ya'yansu a gida. An kuma bada shawarar ma'aikata na iya yin aiki daga gida.