1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Austriya: Za a kafa sabuwar gwamnati

Abdourahamane Hassane
December 16, 2017

Jam'iyyar masu ra'ayin rikau a Austriya tare da jam'iyyar masu kyamar baki sun gabatar da yarjejeniyar da suka cimma ta kafa gwamnati ga shugaban kasar Alexander Van der Bellen.

Österreich Koalitionsverhandlungen ÖVP und FPÖ Strache und Kurz
Hoto: Reuters/L. Foeger

Sebastian Kurz ministan harkokin waje wanda jam'iyyarsa ta ÖVP ta samu nasara a zaben 'yan majalisun dokoki a watan Oktoba. Ya bude shawarwari da jam'iyyar masu kyamar baki ta FPÖ ta Heinz Christian Strache don samun rinjaye don kafa gwamnati. A shekara ta 2000 kungiyar tarrayar Turai ta sakawa Austriya takunkumin karya tattalin arziki bayan da jam'iyyar masu kyamar bakin ta shiga gwamnati.