1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin Iran sun yi tir da shirin Trump

Binta Aliyu Zurmi
January 29, 2020

A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter Ayatollah Ali Khamenei ya ce wannan shiri na shugaba Trump ba yi ba, kuma sauran kasashen musulmi su fito su yi tir da shi.

Iran l Ayatollah Khamenei will Freitagsgebet in Teheran leiten
Hoto: AFP/Iran Press

A Talata ce dai shugaban Amirka Donald Trump ya baiyana shirin na sa, wanda ya tanadi kafa kasar Falasdinawa amma bisa wasu tsauraran sharudda, sannan kuma a bangaren Isra'ila za a ba ta damar mallakar yankuna da dama na gabar yammacin kogin Jordan. 

Tuni shugabanin Falasdinawan suka ki amicewa da shirin wanda suka ce babu adalci a cikin sa.