1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Azumi cikin tsadar rayuwa a Afirka

April 21, 2022

Azumin watan Ramadan a bana ya zo cikin matsanancin hali na tattalin arziki a musanman a kasashen Afirka, abin da ya jefa Musulmi da dama cikin mawuyacin hali.

Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Wasu mazauna kananan yankuna da ke fama da karancin ruwan shaHoto: DW/A. Cascais

Azumin a bana ya zo wa mutane cikin mawuyacin hali na tattalin arziki a duniya, babu ma kamar a kasashe masu tasowa. Baya ga tsadar kayayyaki da karancin ruwan sha, akwai ma matsalar tsananin zafi a galibin kasashen. Matsalolin dai sun fi matsa wa al'umomin kasashe ne irin su Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi inda masu karamin karfi ke kokawa da yadda suke galabaita a sakamakon yanaye-yanayen a bana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna