Gargadi kan yawaitar aure gabnin azumi
March 8, 2022
Masu ba da shawarwari kan zamantakewar aure a Najeriyar dai, sun yi kira ga malamai da sarakunan gargajiya a kan su tashi tsaye domin fargar da ma'aurata kn hatsarin da ke tattare da ire-iren wadannan aure da kuma makomarsa ga zamantakewar al'umma. Sau tari dai a kan samu yawaita yin aure-aue da zarar Watan Ramadan ya karato, sai dai kuma babban abin takaicin shi ne, da zarar an kammala azumin sai auren yai ta mutuwa. Malama Khadijat Sa'ad ita ce shugaban kungiya Babbar Mace Counselling Services a Najeriyar, kungiyar da ta yi fice wajan sulhunta ma'aurata da bayar da shawarwari ga masu shirye-shiryen aure. A cewarta suna samun koke-koken al'umma daga wurare dabam-dabam, dangane da ire-iren wadannan aure da ake yawan yi gabanin gabatowar Azumun Ramadan din.
Wani binciken da tashar DW ta gudanar, ya nunar da cewa wasu da dama na yin auren ne domin kauracewa masu wakar tashe a kan gwaro yayin da wasu kuwa domin cimma wani burinsu ne. Tuni dai malaman addinai da sarakunan gargajiya kamar Malam Shehu Ayatollah Dallatun unguwar Shanu a Kaduna, ke janyo hankalin al'umma kan makomar da jama'ar gari za su fada muddin ba a dauki matakan magance ire-iren wadannan auren ba. A nasu bangaren malaman addinai da sauran masu fafatukar ci-gaban al'umma, tuni suka fara gargadin 'yan kasuwa dangane da irin hatsarin da za su iya jefa alumma sakamakon tsauwala farashin kayayyakin abinci da na masarufi a lokacin azumin.