1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baƙin haure na Siriya a Jamus

November 27, 2013

A kwai baƙin haure kusan dubu 24 'yan ƙasar Siriya da ke zaune Jamus yawancinsu ba bisa ƙaida ba.

Empfänger von WFP-Nahrungsmittelhilfe in Syrien Quelle: WFP
Hoto: WFP

Kimanin 'yan gudu hijira dubu 24 suka fice daga ƙasar Sriya shekarun biyu tun lokacin da aka fara yaƙi a ƙasar domin samun mafuka a nan Jamus a cikin kusan mutane miliyan biyu da rabi da suka fice daga ƙasar. Sai dai fa galibi suna yin balaguro ne cike da haɗari wanda kuma suke bin hanyoyin yin ƙaura mara sa ƙaida inda dama suke mutuwa a kan hayarsu ta tsallakawa daga Turkiya zuwa Girka da farko kafin sun bazu a cikin sauran ƙasashen.

Hukumomin sun gaza dakatar da 'yan gudun hijirar

Masu gadin teku na ƙasar Girka sun yi ta ƙoƙarin takawa 'yan gudun hijirar na Siriya birki waɗanda suka riƙa ratsa tekun yankin cikin jiragen ruwa mara sa inganci daga Turkiya zuwa Girkar. Wadda ke zaman ƙofarsu ta shiga nahiyar Turai kafin a shekarun 2012 a rufe kan iyakar da ke tsakanin Turkiya da da Girka a lokacin kaka amma duk da haka bai hanna komai ba. Wata ƙungiyar da ke fafutukar kare hakin bil adama ta Pro Asyl ta ce tun daga watan Augusta na shekarar ta 2012 'yan gudunn hijira 149 suka mutu daga Turkiya zuwa Girka mataimakin ƙungiyar ta Pro Asyl Bern Mesovic ya ce jama'ar ba su da wani zaɓi.Ya ce :'' A kwai haɗari mafi girma a cikin wanan lamari da 'yan gudun hijirar ke fuskanta ya ce daga cikin waɗanda suka mutu a tekun galibinsu 'yan ƙasar Siriya ne mata haɗe da maza da ke ƙoƙarin tsallaka wa.''

Hoto: Reuters

Gwamnatin ta Jamus ta yi alƙawarin samar da takardun da suka dace na samun moriya da ta dace a hukumce ga 'yan gudun hijirar na Siriya dubu biyar kafin nan da shekarun 2014, to amma hanyoyin da ake bi a samu wannan matsayi na zaɓen waɗanda suka cancanta tare da haɗin gwiwar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD, na kawo jinkiri ga shirin wanda ke tare da sarƙaƙiya. Katrin Göring-Eckardt, wata 'yar majalisar ta jam'iyyar masu fafutukar kare muhali a nan Jamus ta yi tsokaci a kan butun.Ta ce :'' Yakamata da gaggawa gwamnatin Tarrayar Jamus ta fito ƙarara ta gaggauta karɓar 'yan gudun hijira, ta ce duk abin da ya yi saura na ƙaidoji da sauransu a wannan hali da ake ciki ta ce ba ta ganin dalilinsa.''

Yunƙurin gwamnatin Jamus na taimaka wa ' yan gun hijirar

Yawancin ƙasashen da yan gudun hijira ke zuwa kama daga Iraki da Jordan da Libanon da Turkiya har yazuwa nan Jamus akwai ƙaidoji masu tsauri da ake giciyawa 'yan gudun hijirar. Yawanci dai a cikin ƙasashen suna buƙatar dangin 'yan gudun hijira da ke zaune a ƙasar zasu ɗauki ɗawainiyar baƙin. Abu na farko da ke zaman dole sai sun kasance suna da albashi na Euro dubu biyu abin da ke kawo cikas ga ' yan gudun hijirar. Ministan cikin gida na Jamus Hans-Peter Friedrich, ya ce a kwai buƙatar yin wani yunƙuri tare da sauran ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai.

Hoto: Reuters

Ya ce :'' Sai an yi ƙarin rejista na 'yan gudun hijirar ya ce amma ya gabatar da buƙatar ganin an gudanar da wani taron gaggawa na ƙungiyar Tarrayar Turai tare,a ɗauki matakan da suka dace da sauran ƙasaShen domin fuskantar wannan al' amari.'' Kafin dai a kai ga ɗaukar matakan bai ɗaya tsakanin ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai dubban 'yan gudun hijirar ne daga Siriya zasu ci gaba da isa a nahiyar ba kan ƙaida ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe