1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baƙin haure 'yan Afirka a Isra'ila

June 27, 2012

'Yan ci-ranin Afirka a Isra'ila na fuskantar tursasawa daga hukumomin ƙasar saboda rashin cikakkun takardu na izinin zama.

Afrikanische Flüchtlinge in Israel – Jeden Abend um 18 Uhr verteilen Anwohner kostenloses Essen an die Flüchtlinge – im Schnitt 500 bis 700 Portionen. DW/Emilie Baujard
Hoto: DW

A ƙasar Israi'la da sannun a hankali baƙin haure galibi daga nahiyar Afirka masaman ma daga ƙasasashen Sudan da Eritriya inda ake fama da yaƙin basasa na ci gaba da kwarrarawa zuwa ƙasar da nufin samun kyaukyawar rayuwa to sai dai aksarin su, saboda rashin cikkakun takardu na zama suna samun kansu a cikin wani hali na gararanba a birni Tel Avive abinda ke hadasa fushe yahudawa.kuma dangane da haka ne gwamnatin Israi'lan ta soma korar bakin haure .Wannan wani tsohon Park kennnan da akan sayer da motoci na Levinski wanda ke a Tel Aviv, wanda ba shi da nisa da babbar tashar mota ,da a yanzu ya rikiɗe ya koma sansanin yan gudun hijira inda ɗaruruwan jama'a galibi wanda suka zo daga nahiyar afirka suke yi kwanciya.Ga shi yawan su na ƙaruwa kai a kai sannan al 'amuran rayuwa na ci gaba da taɓarɓarewa kamar yadda wani jam'in wata ƙungiyar ta agaji ta Hotiline Migrant Worken ya baiyana

''ya ce ana cikin wani yanayi na ruɗani da ya ce yawancin yan gudun hijira waɗanda basu kan kaida inda su zo nan ake kawo su ;ya ce abin amma mamaki da zaran an ba da belinsu sai a kwashe su a cikin manyan motoci an kai su wani wurin da basu san kowa ba basu kuma da ko sisi kobo sai a ce da su baye baye ya ce tilas su kwana nan.

Garrrarin da yan gudun hijirar ke fuskanta a Isra'ila

Ibrahima wani ɗan ƙasar Sudan ne da ya bar ƙasa watannin biyu da suka wuce domin gujewa yaƙin basasar da ake kuma cikin wannan Park ya ke in barci:''ya ce matsalar shi ne a bisa Pasaseport a rubuta ba mu da izinin yin aiki,shi ne matsalar ga mu a cikin wannan ƙasa amma ba mu da aiki kullum ina kan titi ina jiran wani ya ce ya ɗaukeni aiki.

'Yan gudun hijirar ƙasashen Afirka a Isra'ilaHoto: DW

wasu alƙaluman ƙididiga da gwamnatin Israi'la ta baiyana sun nuna cewar sama da baƙin haure dubu 60 suka shiga Isara'ila a cikin shekaru biyar na baya baya na galibin su daga ƙasashen Sudan da Eritriya kuma sun biyo ne ta tsaunin Sinai da ke a ƙasar Masar wasu sun biyan kusan dala dubu ukkU domin samun shiga.

Dalilai na siysa sun fi ƙarfi akan korar baƙin hauren na Afirka a Isra'ila

Kana da zaran su iso a isaraila babu wasu kungiyoyi masu zaman kanu dake kula da su balantana su ɗauki nauyin su sannan samun matsayin na yan gudun hjira ba ya samuwa nan da nan saboda sai jefi jefi sukan bayar wa Mohammed wani ɗan ƙasar Eritriya ne mai shekara 24 wanda yanzu watan sa guda da zuwa ''ya ce da ina Eritriya cewa ake yi mani Israi'la ƙasa ce mai da daɗi sannan kuma ga kiyaye hakin dimokaradiyya ya ce amma ni na ga ba hakane Isarai'la ba daɗi ya ce ba mutunci, ko repect na yan gudun hijira, ba aiki ba wurin kwanciya duk mutane kan titi suke yi kwanciya.

'Yan gudun hijirar ƙasashen Afirka a Isra'ilaHoto: DW

Wata matsalar daban da bakin hauren yan Afirka su ke fuskanta ita ce ta tashin hankali da ake samu tsakanin al' ummar Israi'la da baƙin wanda suke zargi da aikata kashe kashe na ƙabilanci na jama'a a Tel Avive;abinda jama'ar mai ƙemar baƙi ta ƙasar ke kamanta baƙin da cewa wata Cancer Omar Olivier na daga cikin yan gudun hijirar. ''Ya ce ana saka tsoro a cikin kawunan jama'a ya ce mun juma muna zaune tare da waɗanan mutane amma abinda muke gani yanzu ba a taɓa yi mana shi ba ya ce yan siyasa ne ke ƙara rurura wutar tahin hankalin na ƙemar baƙin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal