Ba a samu sauyi a saman teburin Bundesliga na Jamus ba
April 14, 2025
A gasar Bundesliga ta Jamus, an shiga matakin gudun yada kanin wani, inda kungiyoyi ke rige-rigen samun kyakkyawar makoma bayan da aski ya zo gaban goshi. A wasannin mako na 29, Bayern Munich da babbar abokiyar hamayyarta Borussia Dormund sun tashi 2-2. Ita kuwa Stuttgart ta yi rashin nasara har gida a hannun Werder Bremen da ci 2-1. Eintracht Frankfurt ta lallasa Heidenheim da ci 3-0. Bayer Leverkusen da Union Berlin sun tashi ba kare bin damo wato 0-0.
A jadawalin gasar Bundesliga bayan wasanni 29., Bayern Munich na a matsayin farko da maki 69, yayin da Bayer Leverkusen ke biya mata baya da maki 63. Ita kuwa Eintracht Frankfurt mai maki 51 na a matsayi na uku.
Inda aka kwana a gasar kwallon kafar Ingila
A Firimiyar kasar Ingila kuwa, Newcastle United ta ragargaji Manchester United da ci 4-1. Liverpool ta doke West Ham da ci 2-1. Chelsea da Ipswich Town sun yi kunnen doki 2-2. Wolves ta lafta wa Tottenham kwallaye 4-2. Sannan, bayan wasanni 32, Liverpool na saman teburi da maki 76, yayin da Arsenal ke da maki 63 a matsayi na biyu, ita kuwa Nottingham Forest ke a matsayi na uku da maki 57.
Barcelona na jan zarenta a La Liga na Spain
A La Ligar kasar Spain, a karon farko dan wasan Real Madrid Kylian Mbappe ya ga jan katin kora sakamakon muguntar da ya yi wa dan wasan Alaves Antonio Blanco, ko da yake Real Madrid ta tsira da ci daya da nema da kyar a filin na Alaves. Ita ma Leganes ta sha kashi a gida a hannun Barcelona da ci daya mai ban haushi. A yanzua haka ma bayan wasanni 31 da aka gudanar, Barcelona na kan gaba da maki 70, yayin da Real Madrid ke a matsayi na biyu da maki 66, Ita kuwa Atletico Madrid na da maki 60.
Wasan el classico tsakanin Barcelona da Real Madrid a filin wasa na Nou Camp ranar 11 ga watan Mayu mai kamawa ka iya tantance kungiyar da za ta lashe kambun zakara na gasar ta bana.
Me ake ciki a Serie A na Italiya?
A kasar Italiya wato gasar Serie A, Lazio da Roma sun yi kunnen doki 1-1. Atalanta ta doke Bologna da ci 2-0. Juventus ta casa Lecce da ci 2-1. Yayin da Inter Milan ta lallasa Cagliari da ci 3-1. Amma bayan makonni 32, Inter Milan na kan gaba da 71, yayin da Napoli ke da maki 65 da kwanten wasa daya, ita kuwa Atalanta, tana a matsayi na uku da maki 61.
Nijar na son Badmington ya samu karbuwa
A Jamhuriyar Nijar, an gudanar da gasar wasan Badminton na dalibai 'yan mata na makarantun firamare na birnin Yamai, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na kwadaita wa daliban kaunar wasan, ta hanyar zakulo masu hazaka daga cikinsu don ba su damar shiga babbar kungiyar ta kasa.
Mu leka fagen Tennis
Carlos Alcaraz na kasar Spain ya lashe gasar Monte Carlo Masters bayan casa Lorenzo Musett na Italiya da ci 3-6, 6-1, 6-0. Wannan nasara ta daga likkafarsa zuwa lamba biyu a duniya a jadawalin kwararrun 'yan wasan Tennis da aka fitar . Hakan kuma ka iya ba shi kwarin gwiwar kare kambunsa na French Open a cikin watan Mayu mai zuwa.
Me ake ciki a wasan kwallon lambu?
Shahararren dan wasan kwallon lambu wato Golf Tiger Woods, na kan gaba wajen jinjina wa Rory McIlroy tare da taya shi murnar lashe gasa mafi daraja ta Golf a duniya Masters, a filin wasa na Augusta da ke Amurka. Shekaru goma sha hudu ya yi yana jiran wannan rana. Wannan shi ne karo na karo na 89 na gasar, kuma ya bi sahun fitattun 'yan wasan duniya irin su Tiger Woods, Jack Nicklaus, Gary Player, Ben Hogan da kuma Gene Sarazen.