1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ba a sami ci gaba a tattaunawa kan yakin Gaza ba - Hamas

July 16, 2025

Hamas ta ce har kawo wannan lokaci ba a samu sauyin matsaya a tsakaninta da Isra'ila ba kan daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza wanda bangarorin biyu suka yi watsi da shi a tattaunawar Doha.

Ba bu ci gaban da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
Ba bu ci gaban da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza Hoto: Khames Alrefi/Anadolu/picture alliance

Wani jigo a kungiyar Hamas ya musanta jita-jitar da ake yadawa kan cewa an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi da nufin tsagaita bude wuta a zirin Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa har ma da batun ficewar sajojin Isra'ila baki daya daga yankin Falasdinu.

Karin bayani: An gaza sasanta Isra'ila da Hamas a Qatar

Bassem Naim, kusa a kungiyar mai iko da zirin Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa: ''har yanzu ba bu abin da ya canja dangane da daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta'' wanda bangarorin biyu suka yi watsi da shi a tattaunawar birnin Doha na Qatar, saboda kin aminta da wasu batutuwa ciki har da kwancewa Hamas damara da kuma janye sojojin Isra'ila ga baki daya daga yankin Falasdinu. 

Karin bayani: Isra'ila da Hamas na zargin juna da yin zagon kasa ga shirin tsagaita wuta a Gaza 

A daidai wannan lokaci Hukumar jin kai ta Gaza GHF ta ba da rahoton kisan mutane 20 a wani gurin rabon kayan agaji, tare da zargin wasu mutane dauke da makamai da haddasa hargizi, batun da mahukuntan Falasdinu ke da sabanin ra'ayi a kansa.