Ba bukatar shigar sojin Amurka ta kasa a Iran - Trump
March 6, 2026
Shugaba Donald Trump da ke magana da gidan talbijin na NBC News a daren Alhamis ya ce Iran ta riga ta rasa komai sakamakon lugen wutar da aka yi kanta ya kassara rundunar ruwanta da sauran karfinta na makamai, a don haka a cewarsa, ba bu bukatar Amurka ta kutsa da sojoji ta kasa cikin Iran.
Tasirin yakin Iran kan alakarta da Afirka
Kalaman shugaban na zuwa ne a yayin da ministan harkokin wajen Iran ya zargi Amurkar da shirye-shiryen kai wa Iran harin soja ta kasa don kwace kasar, zargin da Trump din ya bayyana shi a matsayin na 'yan matan amarya.
A ranar Alhamis Shugaba Trump, ya bayyana cewar zai kasance daga cikin wadanda za su zabi wanda zai gaji Ayatollah Khamenei a Iran, a nata bangare Isra'ila ta ce ta kai jerin hare-hare akalla 2.500 kan Iran tun bayan soma fadan.
Jamus ta koka kan rashin sanin makomar Iran bayan yaki
Inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin tsaron Isra'ila kenan Eyal Zamir ya ce "Bayan kammala matakin farko na harin bazata ta sararin samaniya tare da dakile jerin hare-haren makamai masu linzami, a yanzu mun shiga mataki na gaba na aikin kakkabe masu yi mana barazana.