Ukraine ta ki amince wa bukatun Putin
March 21, 2022Shugaba Volodymir Zelensky na Ukraine, ya ce ba gudu-ba-ja da baya a yakin da kasar ke yi da Rasha, ya fadi hakan ne bayan da fadar Kremlin ta nemi ya mika mata ikon biranen Mariupol da Kharkiv kafin ta kawo karshen yakin, Shugaba Vladimir Putin ya gindaya wadannan sharuddan ne a yayin tattaunawa kan mafita daga rikicin da ya janyo salwantan rayuka da dama. A dazun nan Rasha ta mika cikakkun bayanan sojojin Ukraine da ta kama a fagen daga ga Kungiyar agaji ta Red Cross.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya kuwa, ta koka da yadda rikicin ya tagayyara 'yan Ukraine su sama da miliyan shida da rabi da suka rasa matsuguninsu, kamar yadda wani sabon bincike da hukumar ta ce, ta gudanar a farkon wannan watan na Maris ya nunar, António Vitorino, daraktan hukumar mai kula da sashen kaurar jama'a ya kara da cewa, munin lamarin ya zarta hasashe dama tanadin da aka yi don tunkarar bukatun wadanda rikicin ya shafa, akwai wadanda har yanzu ba a iya isar da agaji wuraren da aka tsugunar da su inji jami'in.