Ba gudu ba ja da baya inji Gaddafi
June 23, 2011
Jagoran ƙasar Libiya kanal Mu'ammar Gaddafi yace babu gudu babu jada baya a tirjiyar da yake yi wa dakarun ƙasashen yamma dake luguden wuta don kawar da shi. A wani jawabin da aka watsa ta gidan talavin, Gaddafi yace za ku iya ci gaba da ruguzawa kuna share gidajen mu, amma ba za mu ƙare ba. Gaddafi yace babu sauran sasantawa bayan hallaka yara das jikanin mu. Dole kune za ku jada baya ku pice ba mu ba. Bayan jajantawa wani na hannun damansa wanda aka hallaka iyalansa a harin da sojin NATO suka kai, Gaddafi yace bama tsoro bama neman mafaka ko barin ƙasar mu, tun da mun fahimcina kawar da ƙasar Islama ne manufar ku. Ƙungiyar tsaro ta NATO ta amince jiragen yaƙinta sun kai farmaki a yammacin Tiripoli, amma sun hari wurin soji ne. Yanzu dai an fara samun ɓaraka zakanin ƙungiyar NATO bayan ƙasar Italiya ta bayyana rashin goyon bayan harin NATO duk da cewa ta ƙasar ta ake bi ana kai hare-haren, inda ministan harkokin wajen ƙasar ta Italiya ya buƙaci a tsagaita wuta don ceto fararen hula.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Muhammad Abubakar