Ba mu da kwarin giwa kan Infantio- UEFA
August 6, 2026
Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta ce tana kan bakanta game da barazanar kaurace wa dukkan gasannin FIFA duk da cewa kungiyar ta nemi afuwa kan shirin sayar da hannun jari a gasar Kofin Duniya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, UEFA ta sake jaddada cewa jikinta ya yi sanyi kan shugaban FIFA, Gianni Infantino kuma bata da kwarin gwiwa kansa.
FIFA: Guguwar sauyi na neman tafiya da Infantino
Sanarwar ta ce "kungiyoyin da ke karkashin UEFA sun bayyana cewa akwai sharudda guda biyu kafin su janye matakin kaurace wa gasar FIFA.
Na farko, dole ne a janye shirin sayar da hannayen jari na gasannin kwallon kafa. Na biyu kuma, dole ne a ba da tabbacin cewa ba za a sake yunkurin lalata martabar gasanni ta wannan hanyar ba.
FIFA ta yi amai ta lashe kan shirinta na sayar da hannun jari
A wani abin da ke zama koma baya ga Infantino, kungiyar kwadago ta ‘yan wasan kwallon kafa ta duniya ta zarge shi da amfani da kujerarsa ta hanyar da ba ta dace ba.