Sabuwar gwamnatin Gabon ba ta sake zani ba
January 7, 2026
Fiye da shekara guda bayan hawa mulkin Brice Oligui Nguema, shugaban bai cika alkawurin da ya yi na raba gari da iyalan Bongo ba.
Bayan shekaru 55 na mulkin iyalan Omar Bongo, 'yan Gabon da yawa sun sanya fata ga Brice Oligui Nguema, wato janar da ya hambarar da Ali Bongo Ondimba a ranar 30 ga Agustan 2023 kafin daga bisani ya zama shugaban mulkin farar hula. Galibin 'yan kasar sun so sabon shugaban kasar Gabon ya yi watsi da salon mulkin wadanda suka gabace shi, tare da raba gari kwata-kwata da wadanda aka dama da su a zamanin Bongo. Maimakon haka ya yaki matsalar cin hanci da rashawa, da rashin shugabanci na gari, da son kan da manyan jami'an gwamnati ke yawan nunawa.
Karin Bayani:Kalubalen da Shugaba Oligui zai fuskanta a Gabon
Wasu 'yan Gabon sun yi zaton cewa wannan sauyi zai samu ta hanya samar da sabbin fuskoki a al'amuran gudanar da hakokin gwamnati. Sai dai murnarsu na neman komawa ciki saboda duk da cewa sabbin mutane sun bayyana a siyasance, amma salonsu na kama da na gwamnatin da ta gabata. Ko da shi ma Jonathan Ndoutoume Ngom, malami a fannin siyasa a Jami'ar Libreville kuma tsohon ministan Gabon, yana da irin wannan ra'ayi:
"Salon gudanarwa da aka yi Allah wadai da shi a zamanin gwamnatin da ta fadi, suna ci gaba da samun gindin zama. Wadannan matsaloli sun hada da rashin tsaro, da yaduwar kungiyoyin asiri, da kuma batun satar dukiyar jama'a da ake ci gaba da yi, wanda ba wai kawai ya kebanta ga gwamnatocin Omar Bongo ko Bongo Ali Bongo ba ne kadai."
A cikin gwamnati da kuma a wasu cibiyoyi da masana'antu mallakin gwamnatin Gabon, ana ci gaba da samun mutanen da suka yi aiki a karkashin gwamnatocin da suka gabata, lamarin da ya sa Jonathan Ndoutoume Ngom, malami a fannin siyasa a Jami'ar Libreville kuma tsohon ministan Gabon yin tsokaci a kan wannan batu
Karin Bayani:Gwamnatin mulkin sojan Gabon ta nada majalisa
"Har yanzu muna da wasu fuskoki da muka saba gani, musamman Alexandre Barro Chambrier, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa na Gabon. Shi mutum ne da aka sani tun lokacin Omar Bongo. Ya yi aiki a gwamnatoci daban-daban na Ali Bongo. Akwai kuma Guy-Bertrand Mapangou, tsohon memba na PDG (tsohuwar jam'iyya mai mulki), wanda aka nada shugaban majalisar tattalin arziki da zamantakewa."
Shi kuwa Modeste Abagha Assecko, masanin siyasa, ya ce har yanzu ba a rabu da Bukar ba a harkokin tafiyar da kasa, saboda haka ne ya kamata Shugaba Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a ranar 12 ga Afrilun 2025, ya sauya salon gudanarwa na sojoji da aka san shi da shi zuwa na wanda zai haifar da sakamako ga dubban 'yan Gabon.
" Sauyin ya kasance na dan lokacin kalilan lokacin da aka yi rikon kwarya. Ya kasance zabi mai amfani don halatta mulkinsa. Amma zabin zama shugaba mai karfi maimakon mai bin Yarima a sha kida, da dawowar ministocin tsohuwar gwamnati, sun nuna akasin raba gari da mulki da ya gabata."
Karin Bayani:Yunkurin maido da tsarin mulki a Gabon
Nadin sabuwar gwamnatin Gabon ya zo ne a yanayi na tabarbarewar zamantakewa, inda malaman makarantun firamare da sakandare suka shiga yajin aiki tun ranar 5 ga Janairu, yayin da su kuma ma'aikatan kiwon lafiya suke barazanar dakatar da aiki. A daya hannun kuma, jama'a na ci gaba da tsammanin samun ruwan sha da wutar lantarki. Su kuwa matasan Gabon na jiran mataki mai karfi don yaki da matsalar rashin aikin yi da suke fama da ita.
Sai dai Jonathan Ndoutoume Ngom, ya ce duk da ci-gaban mai hakar rijiya da ake samu a Gabon, akwai wasu nasarorin da za a iya danganta su da Shugaba Brice Oligui Nguema.
"An samu ci gaba a fannin wasu kayayyakin more rayuwa a Libreville da kuma cikin jihohin kasar. An kuma samu canje-canje a harkokin shugabanci, duk da cewa wasu tsofaffin halaye na ci gaba da wanzuwa. Sanin kowa na cewar ba za a iya cike gibin shekaru 14 ko 56 a cikin shekaru biyu ba."
Tsammani na ci gaba da wakana a kan sabuwar majalisar ministocin Gabon don kiyaye zaman lafiya da inganta tattalin arziki, ta hanyar daukar mataki mai tasiri kan tsadar rayuwa tare da inganta rayuwar yau da kullun ta 'yan kasar Gabon.