Babu batun Sallar idi bana a fadin Najeriya
May 23, 2020
A wata sanarwa da ya fitar sarkin Musulmin Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na uku kuma shugaban kungiyar Jama'atul Nasril Islam ka na shugaban majalisar koli akan harkokin addinin Islama a Tarayyar ta Najeriya, ta hannun sakataren kungiyar ta (JNI) Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya bayyana dakatar da gudanar da Sallar Idi a dukkanin garuruwa da birane da ke fadin kasar.
A cikin sanarwar sarkin ya bukaci al’ummar Musulami a Najeriya da su gudanar da Sallar Idin a gidajensu tare da iyalansu, ko kuma su kadai. Sanarwar ta ce jihohin da suka cimma matsaya za su gudanar da Sallar Idin a Masallatai bisa shawarwarin kwararru ta banagaren lafiya, to su tabbatar sun dauki matakan amfani da takunkumi da kuma bayar da tazara tsakanin juna kana su kuma yi anfani da man wanke hannu wato Sanitizer domin kare lafiyar al'umma.
Daga karshe sanarwar ta bukaci malammai da suji tsoron Allah a dukkanin lamuransu, yayin da su kuma Musulami a Najeriya ta yi kira da su ci gaba da gudanar da kyawawan ayyuka da suka koya a lokacin azumin Ramadana. Tuni dai malamman Addinin Islama ke ganin hana Sallar Idin ba wai wani sabon abu ba ne a tarihin Musulunci. A karshen mako ne dai ake sa tran Musulmai za su kammala azumin Radanan na bana, da aka shafe tsawon makonni hudu ana yi.