Ba za a yi zabe bana a Jamhuriyar Kongo ba
July 10, 2017Talla
Shugaban hukumar zaben Corneille Nangaa ya shaidawa manema labarai a Kinshasa babban birnin kasar cewa zai yi matukar wuya a iya gudanar da zaben kafin watan Disamba.
A karshen wannan shekarar ce dai ya kamata a gudanar da zaben bisa yarjejeniyar da aka cimma domin kaucewa tashin hankali bayan da shugaban kasar Joseph Kabila da ya dade a karagar mulki yaki amincewa ya sauka a karshen wa'adin mulkinsa a watan Disambar bara.
Jami'yyun adawa sun soki lamirin matakin da cewa tamkar wata takalar fada ce da kuma daure wa gwamnatin gindin cigaba da zama a karagar mulki.