1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

"Ba za mu dena kera makaman nuclear ba" - Kim Jong Un

Abdul-raheem Hassan
March 24, 2026

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya jaddada matsayarsa na karfafa makaman kare dangi na dindindin, ya kuma kwatanta makwabciyarsu Koriya ta Kudu a matsayin babban makiya.

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong UnHoto: Korea News Service/AP/picture alliance

Da yake magana a wani muhimmin zama na majalisar dokoki a Pyongyang, Kim ya ce Koriya ta Arewa za ta ci gaba da karfafa makamanta na nukiliya tare da kawar da duk wata tattaunawa nan gaba da nufin hana su amfani da makaman. Ya bayyana ikon nukiliya a matsayin mai mahimmanci ga tsaron kasa da kuma tasirin gwamnati.

Kim ya yi Ya yi watsi da ra'ayin cewa kwance damarar makaman nukiliya na iya zama silar habaka tattalin arziki ko tabbacin tsaro, yana mai cewa kan mage ya waye, girka makaman nukiliya yayin da kasar ke habaka, shi ne mafita mai bullewa.