Iran ta dage kan ci gaba da inganta shirinta na nukiliya
July 22, 2025
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa Teheran ba za ta yi watsi da shirinta na nukiliya ba, musamman ma inganta makamashin uranium duk da irin barnar da Amurka ta yi wa cibiyoyinta a watan da ya gabata.
A cikin wata hira da ya yi da kafar talabijin ta Fox News, Araghshi ya ce: ''ko da shi ke a halin yanzu an dakatar da wannan shirin saboda barna mai yawa da harin Amurka ya haddasa a cibiyoyin, amma kuma ba za a yi watsi da wannan gagarumar nasara da kasar ta samu a fannin kimiya ba.''
Karin bayani: Iran da wasu kasashen Turai na shirin zama a Turkiyya kan shirin nukiliyar Teheran
Kalaman jami'in diflomasiyyan na Iran na zuwa ne a daidai lokaci da Teheran ke shirin gudanar da sabuwar tattaunawa da kasashen Jamus da Faransa da kuma Burtaniya kan shirinta na nukiliya a birnin Istambul na Turkiyya a Juma'a mai zuwa domin cimma masalaha cikin ruwan sanhi.
A ranar Asabar da ta gabata dai shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada cewa an lalata dukannin tasoshi nukiliyar Iran uku da aka wa hari a watan Yuni da ya gabata sannan kuma ya yi bazanar sake kai wani hari muddin Teheran ta yi kokarin sake farfado da wadannan cibiyoyi.