1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Babban bankin Najeriya ya sake yin karin kudin ruwa

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
March 27, 2024

A Najeriya ana martani a kan matakin babban bankin kasar na sake kara kudin ruwa da ake biya a cikin kasar, a kokari na shawo kan hauhawan farashi da koma bayan tattalin arziki da ake ciki.

Naira kudin Najeriya
Naira kudin NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A Najeriya ana martani a kan matakin da babban bankin kasar ya dauka na sake kara kudin ruwa da ake biya a cikin kasar, a kokari na shawo kan hauhawan farashin kayayyaki da koma bayan tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.

Karo na biyu ke nan a jere, babban bankin Najeriyar na kara kudin ruwa a cikin kasar, inda a wannan karon karin da aka yi zuwa kashi 24.75 daga kashi 22.75 da aka yi a cikin kasa da wata guda. Wannan dai mataki ne da ake dauka a kokari na shawo kan mumunar matsalar hauhawan farashin kayayyaki a cikin Najeriyar tare da fatan ta farfado da darajar Naira.

Gwamnan Babban bankin Najeriyar, Olayemi Cardoso ya ce abin da kwamiti mai kula da manufofin tattalin arziki ya yi la'akari da shi kafin daukar matakin, ya maida hankali ne a kan matsaloli na hauhawan farashin kayayyaki tare da duba mahangar wannan ta yadda za a samu daidaito a alkaluman kudin ruwa. Don haka don a samu daidaito na farashi dole ne a dauki wasu matakai, ta yadda mai saye da sayarwa zai samu walawa.

Tuni dai kungiyar masu masana'antu ta Najeriya ta yi kashedin cewa karin kudin ruwa da aka yi zai jefa harkar masana'antu cikin mawuyacin hali tare da fuskantar rage ma'aikata. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da wasu kamfanoni suka rage ma'aikata wasu kuma suka bar Najeriyar.

Tun bayan kama aikinsa, gwamnan babban bankin Najeriyar ke ta bullo da sabbin manufofi a kokari na maido da darajar Naira wacce a makon nan aka fara ganin sauyi tare da raguwar farashin wasu kayayyakin abinci a kasar.