Babban Hafsan Sojin Libya ya rasu a hadarin jirgin sama
December 24, 2025
Babban Hafsan Sojin Libya Muhammad Ali Ahmad al-Haddad ya rasu a hadarin jirgin sama a Turkiyya a ranar Talata da maraice.
Jirgin saman da ke dauke shi da kuma wasu jami'an soji ya bayar da rahoton samun matsalar lantarki tare da neman sauka cikin gaggawa, jim kadan kafin ya yi hadari a kusa da Ankara a cewar hukumomi.
Sojojin Turkiyya 20 sun rasu a hadarin jirgin sama
Shugaban sashen sadarwa na Turkiyya ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin da ake jiran bayanai kan hadarin jirgin saman.
A cewar wata sanarwa da Burhanettin Duran ya fitar, jirgin Dassault Falcon 50 ya tashi daga filin jirgin sama na Esenboga a Ankara da karfe 17:17 GMT a ranar Talata, yana kan hanyarsa ta zuwa Tripoli.
Da ƙarfe 17:33 GMT, jirgin ya sanar da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama cewa ya samu matsalar gaggawa sakamakon tangardar lantarki.
Rahotanni daga jami’an Libya da na Turkiyya sun ce mutane takwas, ciki har da ma’aikatan jirgin uku, sun rasu a hadarin.
Hadarin jirgin saman Kenya ya halaka dukkan mutanen cikinsa
Masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun juya jirgin ya koma filin jirgin saman Esenboga, sai dai jirgin ya bace daga na'urar hange da ƙarfe 17:36 GMT yayin da yake kokarin yin saukar gaggawa.