1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fara koran jami'in ICE daga Minneapolis

Abdul-raheem Hassan
January 27, 2026

Babban jami'in kula da iyakoki Gregory Bovino zai bar birnin Minneapolis, bayan tsananin zanga-zangar adawa da ayyukan jami'an shige da fice. Bovino na kan gaba wajen tabbatar da manufar Trump na yaki da bakin haure.

Gregory Bovino, babban jami'in ICE a Minneapolis
Gregory Bovino, babban jami'in ICE a MinneapolisHoto: Steven Garcia/NurPhoto/picture alliance

Hukumomi Minneapolis sun tabbatar da janye karin wasu jami'an ICE daga birnin nan ba da jimawa ba, matakin na zuwa ne bayan kashe ma'aikaciyar jinya mai shekaru 37 'yar kasar Amurka a Minneapolis.

Kisan ya kara tsamin dangantaka tsakanin hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya da al’umma a birnin Minneapolis, wanda tuni ke daukar hankali na zama birni mai hatsari ga bakin haure. A ranar 7 ga watan Janairun 2026, jami’an shige da fice sun harbe wata mata har lahira a cikin motarta.