Babban sakataran MDD ya yi jawabi akan Siriya
January 15, 2012Babban sakataran MDD Ban Ki Moon ya buƙaci shgaban ƙasar Siriya da ya kawo ƙarshen kisan gilar da ya ke aikata wa kan al'ummar sa ''ya ce a yau na ƙara jadada cewar da shugaba Bashar Al Assad da ya dakatar da kisan jama´ar sa,
Ya ce kuma tarihi ya nuna cewar babu wani shugaba da ya riƙa amfani da ƙarfin dawo dawo akan al´ummar sa kana kuma ya sha salin alin.Mista Ban Ki Moon wanda ya baiyana haka a wajan wani taro a birnin Berouthe na ƙasar Libanon wanda ke tattauna sauye sauyen da kuma yadda za a riƙa tafiyar da gwamntin wucin gadi ta dimokariyya wanda tsafin shugabannin ƙasashen duniya da kuma masu ci yanzu suke hallarta ya ce lokaci yayi da za a samu sauyi a Siriya.Wannan furci da babban sakataran majalisar ya yi ,ya zo ne a daidai lokaci da shugaba Assad ya baiyana wani ƙudirin doka ;da yayi ahuwa ga waɗanda ke da hannu a cikin yamutsin da aka soma a ƙasar tun cikin watan maris da ya gabata.
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal